Ayu 19:27-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Zan gan shi ido da ido,Ba kuwa zai zama baƙo a gare ni ba.“Zuciyata ta karai saboda ku mutane kun ce,

28. ‘Ta ƙaƙa za mu yi masa azaba?’Kuna neman sanadin da za ku fāɗa mini.

29. Amma yanzu, sai ku ji tsoron takobi,Ku ji tsoron takobin da yake kawo hasalar Allah a kan zunubi.Don haka za ku sani akwai wani mai yin shari'a.”

Ayu 19