4. Ka baƙantar da hankalinsu, ya Allah,Kada ka bar su su yi mini duban wulakanci yanzu.
5. A karin maganar mutanen dā an ce,‘Kowa ya ci amanar abokinsa saboda kuɗi,'Ya'yansa sā sha wahala!’
6. Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.Da mutane suka ji,Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.
7. Baƙin cikina ya kusa makantar da ni,Hannuwana da ƙafafuna sun rame,sun zama kamar kyauro.
8. Duk waɗanda suka zaci su adalai ne sun razana.Dukansu sun kāshe ni, cewa ni ba mai tsoron Allah ba ne.