10. Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa.Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.
11. Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci,Haka nan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi.
12-13. “Tsofaffi suna da hikima,Amma Allah yana da hikima da iko.Tsofaffi suna da tsinkaya,Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.
14. Sa'ad da Allah ya rurrushe, wa zai iya sāke ginawa?Wa kuma zai iya fitar da mutumin da Allah ya sa a kurkuku?
15. Akan yi fari sa'ad da Allah ya hana ruwan sama,Rigyawa takan zo sa'ad da ya kwararo ruwa.
16. Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yakeDa macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.
17. Yakan mai da hikimar masu mulki wauta,Yakan mai da shugabanni marasa tunani.