54. Da suka ji haka, suka husata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa.
55. Amma Istifanas, a cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya zuba ido sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye a dama ga Allah.
56. Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”
57. Amma suka ɗauki ihu ƙwarai, suka tattoshe kunnuwansu, suka aukar masa da nufi ɗaya,
58. suka fitar da shi a bayan gari suka yi ta jifansa da dutse. Shaidu kuwa suka ajiye tufafinsu wurin wani saurayi, wai shi Shawulu.