6. Su kuwa suna zaton wurin zai kumbura, ko kuwa farat ɗaya ya fāɗi matacce. Amma da aka daɗe suka ga ba abin da ya same shi, suka sāke magana suka ce lalle shi wani Allah ne.
7. A nan kusa kuwa akwai wani fili, mallakar shugaban tsibirin nan, mai suna Babiliyas. Shi ne ya karɓe mu, ya sauke mu a cikin martaba har kwana uku.
8. Ashe, uban Babiliyas yana a kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu'a, ya ɗora masa hannu ya warkar da shi.
9. Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkar da su.
10. Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da muke bukata.
11. Bayan wata uku muka tashi a cikin wani jirgin Iskandariya, wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwaye Maza.
12. Da muka zo Sirakusa muka kwana uku a nan.
13. Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana, iska ta taso daga kudu, kashegari kuma muka kai Butiyoli.
14. A nan muka tarar da waɗansu 'yan'uwa, suka roƙe mu mu kwana bakwai tare da su. Da haka dai har muka isa Roma.