14. Ba da jimawa ba kuwa sai ga wata gawurtacciyar iska da ake kira Yurokilidon ta bugo daga tsibirin.
15. Da iskar ta bugo jirgin, har ya kasa fuskantarta, sai muka sallama mata, ta yi ta kora mu.
16. Da muka bi ta jikin wani ɗan tsibiri wai shi Kauda muka samu muka yi iko da ƙaramin jirginmu da ƙyar.
17. Bayan suka jawo ƙaramin jirgi ɗin a cikin babban jirgi, sai suka yi dabara suka ɗaɗɗaura igiyoyi ta gindin babban jirgin, suka rage shi. Don kuma gudun kada a fyaɗa su a yashin nan na Sirtis mai haɗiye kome, suka sauke filafilai, aka kora jirgin haka.