A.m. 23:19-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sai shugaban ya kama hannun saurayin, ya ja shi a waje ɗaya, ya tambaye shi a keɓance, “Wace magana za ka gaya mini?”

20. Yaron ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kai musu Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincika maganarsa sosai.

21. Amma kada ka yardar musu, don fiye da mutum arba'in daga cikinsu suna fakonsa, sun kuma yi rantsuwa a kan ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye suke, yardarka kawai suka jira.”

22. Sai shugaban ya sallami saurayin ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka sanar da ni maganar nan.”

23. Sa'an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba'in, da 'yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.”

24. Ya kuma yi umarni su shirya wa Bulus dabbobin da zai hau, don su kai shi wurin mai mulki Filikus lafiya.

25. Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka:

A.m. 23