A.m. 16:27-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Da yāri ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa yake 'yan sarƙa sun gudu.

28. Amma Bulus ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Kada ka cuci kanka, ai duk muna nan!”

29. Sai yari ya ce a kawo fitilu, ya yi wuf ya ruga ciki, ya fāɗi gaban Bulus da Sila, yana rawar jiki don tsoro.

A.m. 16