25. Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’
26. “Ya ku 'yan'uwa, zuriyar Ibrahim, da kuma sauran masu tsoron Allah a cikinku, mu fa aka aiko wa kalmar ceton nan.
27. Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa'an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi.
28. Ko da yake ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi.
29. Da suka cikasa dukkan abin da aka rubuta game da shi, suka sauko da shi daga kan gungumen, suka sa shi a kabari.
30. Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31. Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushalima daga Galili, waɗanda a yanzu su ne shaidunsa ga jama'a.
32. Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,
33. ya cika mana shi, mu zuriyarsu, da ya ta da Yesu daga matattu, yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,‘Kai Ɗana ne,Ni Ubanka ne yau.’
34. Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi, a kan cewa ba zai sāke komawa cikin halin ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce,‘Zan yi muku tsattsarkar albarkar nan da na tabbatar wa Dawuda.’
35. Domin a wata Zabura ma ya ce,‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
36. Dawuda kam, bayan da ya bauta wa mutanen zamaninsa bisa ga nufin Allah, ya yi barci, aka binne shi tare da kakanninsa, ya kuwa ruɓe.
37. Amma shi wannan da Allah ya tashe shi, bai ruɓa ba.
38. Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.
39. Ta gare shi kuma, duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukan abubuwan da ba dama Shari'ar Musa ta kuɓutar da ku.