4. Da ya kama shi, ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, su yi tsaronsa, da niyyar kawo shi a gaban jama'a bayan idin.
5. Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, Ikkilisiya kuwa ta himmantu ga roƙon Allah saboda shi.
6. A daren da in gari ya waye Hirudus yake da niyyar fito da shi a yi masa hukunci, Bitrus kuwa na barci a tsakanin soja biyu, ɗaure da sarƙa biyu, masu tsaro kuma suna bakin ƙofa suna tsaron kurkukun,
7. sai ga mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka ɗakin, sa'an nan mala'ikan ya bugi Bitrus a kwiɓi, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sarƙar ta zube daga hannunsa.