Afi 3:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,

6. wato, yadda ta wurin bishara al'ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.

7. An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa.

8. Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,

9. in kuma bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa.

10. An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.

Afi 3