2 Tim 1:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.

8. Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,

9. wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil'azal, a cikin Almasihu Yesu,

10. wadda a yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai Cetonmu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara.

2 Tim 1