1. To, a game da komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma taruwarmu mu sadu da shi, muna roƙonku 'yan'uwa,
2. kada ku yi saurin jijiguwa a zukatanku, ko kuwa hankalinku yă tashi, saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu suke, cewa ranar Ubangiji ta zo.