2 Tar 9:29-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Sauran ayyukan Sulemanu daga farko har ƙarshe an rubuta su a tarihin annabi Natan. An kuma rubuta su a annabcin Ahaija Bashilone, da kuma a wahayin Iddo maigani, game da Yerobowam ɗan Nebat.

30. A Urushalima, Sulemanu ya yi shekara arba'in yana mulkin dukan Isra'ila.

31. Sulemanu ya rasu aka binne shi tare da kakanninsa a birnin tsohonsa Dawuda, Rehobowam ɗansa shi ya gāje shi.

2 Tar 9