16. Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’
17. Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.
18. “Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.
19. Duk da haka ka kula da addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu'ar da bawanka yake yi a gabanka.