20. Sai sarki Hezekiya, da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu'a saboda wannan al'amari, suka yi kuka zuwa Sama.
21. Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.
22. Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mazaunan Urushalima daga hannun Sennakerib Sarkin Assuriya, daga kuma hannun dukan maƙiyansa, ya hutar da su ta kowace fuska.
23. Mutane da yawa suka kawo wa Ubangiji sadakoki a Urushalima, suna kuma kawo wa Hezekiya Sarkin Yahuza abubuwa masu daraja. Saboda haka ya sami ɗaukaka a idon dukan sauran al'ummai, tun daga wannan lokaci har zuwa gaba.