2 Tar 3:3-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ga awon harsashin da Sulemanu ya kafa domin ginin Haikalin Ubangiji. Tsawonsa bisa ga tsohon magwajin, kamu sittin ne, fāɗin kuwa kamu ashirin.

4. Tsawon shirayi daga gaban Haikalin ya yi daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, sa'an nan tsayinsa kamu ɗari da ashirin. Aka shafe ciki da zinariya tsantsa.

5. Ya jera itatuwan fir a cikin babban ɗakin, sa'an nan ya shafe su da zinariya tsantsa, ya kuma zana siffofin itatuwan dabino da na sarƙoƙi.

6. Banda wannan kuma ya ƙawata Haikalin da duwatsu masu daraja da zinariya irin ta Farwayim.

2 Tar 3