13. Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban ɗakin.
14. Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa'an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.
15. Ya kuma yi ginshiƙai biyu domin ƙofar Haikalin, tsayinsu kamu talatin da biyar ne, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.