6. Sai sarki ya kira Yehoyada babban firist, ya ce masa, “Don me ba ka sa Lawiyawa su tafi Yahuza, da Urushalima, su karɓo kuɗin da Musa, bawan Ubangiji, ya aza wa taron jama'ar Isra'ila su kawo domin alfarwar sujada ba?”
7. Gama 'ya'ya maza na Ataliya, muguwar matan nan, sun kutsa kai a cikin Haikalin Ubangiji, suka yi amfani da dukan tsarkakan kayayyakin Haikalin Ubangiji domin gumaka.
8. Don haka sai sarki ya ba da umarni, a yi babban akwati, a ajiye shi a waje a ƙofar Haikalin Ubangiji.
9. Sai aka yi shela a Yahuza da Urushalima, a kawo wa Ubangiji kuɗin da Musa, bawan Allah, ya aza wa Isra'ila sa'ad da suke cikin jeji.
10. Sai dukan sarakuna, da dukan jama'a, suka yi farin ciki, suka kawo kuɗin da aka aza musu, suka zuba a babban akwatin, har ya cika.
11. Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa 'yan majalisar sarki babban akwatin sa'ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na'ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da suke cikin babban akwatin, sa'an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.