1. Sai Sulemanu ya yi niyya a ransa zai gina Haikali saboda sunan Ubangiji, ya kuma gina wa kansa fāda.
2. Don haka, sai ya sa mutane dubu saba'in (70,000) don ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) su haƙo duwatsu a tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuma su ne shugabanni.
3. Sulemanu fa ya aika wurin Hiram Sarkin Taya ya ce, “Yadda ka yi wa tsohona Dawuda, wato ka aiko masa da itatuwan al'ul domin ya gina gida inda zai zauna, ni ma ina so ka yi mini haka.