2 Tar 19:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai ya naɗa alƙalai a ƙasar, a dukan biranen Yahuza masu kagara, birni birni.

6. Sai ya ce wa alƙalan, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari'ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa'ad da kuke yanke shari'a.

7. Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”

8. Yehoshafat kuma ya naɗa waɗansu Lawiyawa, da firistoci, da waɗansu shugabannin iyalan Isra'ilawa, saboda su yi shari'a tsakani da Ubangiji, su daidaita tsakanin masu jayayya. A Urushalima za su zauna.

9. Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma.

2 Tar 19