4. Yehoshafat ya yi zamansa a Urushalima, ya sāke shiga jama'a, tun daga Biyer-sheba har zuwa ƙasar tuddai ta Ifraimu, ya komar da su zuwa wurin Ubangiji, Allah na kakanninsu.
5. Sai ya naɗa alƙalai a ƙasar, a dukan biranen Yahuza masu kagara, birni birni.
6. Sai ya ce wa alƙalan, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari'ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa'ad da kuke yanke shari'a.