1. Yehoshafat ɗansa kuwa ya gāji gadon sarautarsa, ya kahu sosai gāba da Isra'ila.
2. Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi.
3. Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat saboda ya bi halin tsohonsa da ya yi da fari, bai kuwa nemi Ba'al ba.
4. Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra'ila ba.