3. Isra'ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari'a.
4. Amma lokacin da suke shan wahala suka juyo ga Ubangiji Allah na Isra'ila, suka neme shi, suka same shi.
5. A waɗancan lokatai, ba salama ga mai fita ko ga mai shiga, gama babban hargitsi ya wahalar da dukan mazaunan ƙasashe.
6. An kacancana su, al'umma tana gāba da al'umma, birni kuma gāba da birni, gama Allah ya yi ta wahalshe su da kowace irin wahala.
7. Amma ku sai ku yi ƙarfin hali, kada ku firgita, gama za a ba ku ladan aikinku.”
8. Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa'an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.
9. Sai ya tattara dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, da kuma na Ifraimu, da na Manassa, da na Saminu, waɗanda suke zaman baƙunci tare da su. Da yawa daga cikin Isra'ilawa suka yi ƙaura zuwa wurinsa, sa'ad da suka ga Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
10. Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta sarautar Asa.
11. A ran nan suka miƙa wa Ubangiji hadayun bijimai ɗari bakwai, da tumaki dubu bakwai (7,000) daga cikin ganimar da suka kwaso.
12. Sai suka ƙulla alkawari, cewa za su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu da dukan zuciyarsu da ransu.
13. Duk wanda kuma bai nemi Ubangiji, Allah na Isra'ila ba, za a kashe shi, ko yaro ko babba, ko mace ko namiji.
14. Sai suka rantse wa Ubangiji da murya mai ƙarfi, suna sowa, suna busa kakaki da ƙaho.
15. Dukan Yahuza ta yi murna saboda rantsuwar, gama da zuciya ɗaya suka rantse, suka kuwa neme shi da iyakar aniya, sun kuwa same shi. Don haka Allah ya hutasshe su a kowane al'amari.