2 Tar 15:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Azariya ɗan Oded,

2. sai ya fita ya taryi Asa, ya ce masa, “Ka ji ni, ya Asa, kai da dukan Yahuza da Biliyaminu, Ubangiji yana tare da ku idan kuna tare da shi. Idan kuwa kun neme shi, za ku same shi, amma idan kun rabu da shi, shi ma zai rabu da ku.

3. Isra'ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari'a.

4. Amma lokacin da suke shan wahala suka juyo ga Ubangiji Allah na Isra'ila, suka neme shi, suka same shi.

2 Tar 15