2. Asa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.
3. Ya kawar da baƙin bagadai da masujadai, ya rurrushe ginshiƙai, ya kuma tumɓuke Ashtarot.
4. Ya umarci Yahuza su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kiyaye doka, da umarni.
5. Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagadan ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa.
6. Ya giggina birane masu kagara a Yahuza, gama ƙasar tana zaman lafiya. A waɗannan shekaru bai yi yaƙi da kowa ba, saboda Ubangiji ya kawo masa salama.