2 Tar 11:14-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da 'ya'yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji.

15. Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.

16. Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, daga kowace kabilar Isra'ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.

2 Tar 11