Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Hamutal 'yar Irmiya na Libna.