Ya kuma lalatar da matsafai na kan tuddan da suke gabashin Urushalima, kudu da Dutsen Hallaka, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya gina wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh gunkin Mowab, da Milkom gunkin Ammonawa.