2 Sar 22:18-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Amma a kan Sarkin Yahuza, wanda ya aiko ku, ku tambayar masa Ubangiji, ku faɗa masa Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A kan maganar da ka ji,

19. da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa'ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la'ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka.

20. Domin haka, ba za ka ga hukuncin da yake zuwa a kan Urushalima ba, za a kai ka cikin kabarinka lafiya.’ ”Mutanen kuwa suka mayar wa sarki Yosiya da wannan magana.

2 Sar 22