2 Sar 21:3-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba'al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu.

4. Ya gina bagadai a Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima zan sa sunana.”

5. Ya gina wa taurarin sama bagadai a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji.

6. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma'amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

2 Sar 21