17. Sarki Ahaz kuwa ya yanke sassan dakalan, ya ɗauke daruna da suke bisansu, ya kuma ɗauke kwatarniya da take bisa bijimai na tagulla, ya ajiye kwatarniya a daɓen dutse.
18. Hanyar da aka killace ta Asabar, wadda suka yi a cikin gidan, da ƙofar waje ta shigar sarki, Ahaz ya kawar da su daga Haikalin Ubangiji saboda Sarkin Assuriya.
19. Sauran ayyukan Ahaz waɗanda ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
20. Ahaz ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Sai ɗansa, Hezekiya, ya gaji sarautarsa.