25. Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.
26. Sauran ayyukan Fekahiya, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
27. A shekara ta hamsin da biyu ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Feka ɗan Remaliya ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara ashirin.
28. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
29. A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.