2 Sar 11:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Da Ataliya ta ji muryoyin matsara da na jama'a, sai ta zo wurin mutane a Haikalin Ubangiji.

14. Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”

15. Yehoyada, firist kuwa, ya umarci shugabannin sojoji, ya ce, “Ku fitar da ita daga nan, duk kuma wanda yake son kāre ta, ku sa takobi ku kashe shi.” Ya kuma ce, “Kada a kashe ta a Haikalin Ubangiji.”

16. Suka kama ta, suka fitar da ita ta ƙofar dawakai zuwa gidan sarki, can suka kashe ta.

17. Yehoyada kuwa ya yi alkawari tsakanin Ubangiji, da sarki, da jama'a, yadda za su zama jama'ar Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da jama'a.

2 Sar 11