2 Sar 10:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ahab yana da 'ya'ya maza saba'in a Samariya, sai Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika zuwa Samariya wurin shugabanni da dattawan birni, da masu lura da 'ya'yan Ahab.

2. Ya ce, “Yanzu dai, da zarar wasiƙun nan sun iso wurinku, da yake kuke lura da 'ya'yan Ahab, kuna kuma da karusai, da dawakai, da kagara, da makamai,

3. sai ku zaɓi wanda ya fi dacewa duka daga cikin 'ya'yan Ahab, ku naɗa shi sarki, ku yi yaƙi, domin ku tsare gidan Ahab.”

4. Amma suka ji tsoro ƙwarai, suka ce, “Ga shi, sarakuna biyu ba su iya karawa da shi ba, balle mu.”

2 Sar 10