15. Amma ba zan daina nuna masa madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na yi wa Saul wanda na kawar daga fuskata.
16. Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”
17. Haka kuwa Natan ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
18. Sarki Dawuda ya tafi ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ko ni ko iyalina ba mu cancanci dukan abin da ka yi mana ba.
19. Ga shi, ka ƙara fiye da haka, ya Ubangiji Allah, gama ka yi magana, cewa, gidan bawanka zai kai kwanaki masu tsawo. Wannan ka'ida ce ta 'yan adam!
20. Me kuma zan ƙara ce maka, gama ka san bawanka, ya Ubangiji Allah.
21. Bisa ga alkawarinka da yardar zuciyarka ne ka aikata waɗannan manyan al'amura domin ka sa in san su.
22. Bisa ga dukan abin da muka ji, kai mai girma ne, ya Ubangiji Allah. Ba kamarka, in banda kai kuma babu wani Allah.
23. Ba wata al'umma kuma a duniya wadda take kama da jama'arka Isra'ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama'arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama'arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al'ummai da gumakansu a gaban jama'arka, waɗanda ka fansa daga Masar.
24. Ka zaɓar wa kanka jama'ar Isra'ila su zama mutanenka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
25. “Ya Ubangiji Allah, yanzu ka tabbatar da maganar da ka yi da bawanka da gidansa har abada. Ka aikata bisa ga faɗarka.
26. Za a kuwa ɗaukaka sunanka da cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila har abada.’ Gidan bawanka Dawuda kuma zai kahu a gabanka.