10. sa'ad da wani ya kawo mini labari cewa, ‘Saul ya mutu,’ mutumin ya yi tsammani albishir ne ya kawo mini, sai na kama shi na kashe shi a Ziklag. Ladan da na ba shi ke nan saboda labarinsa.
11. Balle fa ku da kuke mugayen mutane, da kuka kashe adali a gadonsa, a cikin gidansa, ba sai in nemi hakkin jininsa a hannunku ba, in kawar da ku daga duniya?”
12. Sai Dawuda ya umarci samarinsa su kashe su. Suka datsa hannunsu da ƙafafunsu, suka rataye su a gefen tafkin Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-boshet suka binne a cikin kabarin Abner a Hebron.