33. Allahn nan shi ne mafaka, mai ƙarfi ne a gare ni,Ya sa hanyata ta zama lafiyayyiya.
34. Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa,Ya kiyaye ni a kan duwatsu.
35. Ya horar da ni domin yaƙi,Domin in iya tausa baka mafi ƙarfi.
36. “Ya Ubangiji, ka kiyaye ni, ka cece ni,Taimakonka ya sa na zama babba.
37. Ka hana a kama ni,Ban kuwa taɓa faɗuwa ba.
38. Na runtumi abokan gābana, na kuwa hallaka su,Ban tsaya ba sai da na kore su.
39. Na fyaɗa su ƙasa, ba su iya tashi ba,Suna kwance warwar a ƙafafuna.
40. Ka ba ni ƙarfi domin yin yaƙi,Nasara kuma a kan abokan gābana.
41. Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana,Na hallaka waɗanda suke ƙina.
42. Suka nemi taimako, amma ba wanda zai cece su,Suka yi kira ga Ubangiji, amma bai amsa musu ba.
43. Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura,Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.