2 Sam 22:19-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sa'ad da nake cikin wahala sun auka mini,Amma Ubangiji ya kiyaye ni.

20. Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari,Ya cece ni domin yana jin daɗina.

21. “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina,Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.

22. Gama na kiyaye dokar Ubangiji,Ban yi wa Allahna tayarwa ba.

2 Sam 22