1. Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”
2. Sai dukan Isra'ilawa suka janye jiki daga wurin Dawuda, suka bi Sheba, ɗan Bikri, amma mutanen Yahuza suka manne wa sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.
3. Da Dawuda ya koma gidansa a Urushalima, kwarakwaran nan nasa guda goma waɗanda ya bar su tsaron gida ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya yi ta lura da su, amma bai shiga wurinsu ba. Haka suka zauna a keɓe, suna zaune kamar gwauraye.
4. Sa'an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mini mutanen Yahuza kafin kwana uku, kai kuma ka zo tare da su.”