16. Shimai ɗan Gera kuma, mutumin Biliyaminu daga Bahurim, ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuza don ya taryi sarki Dawuda.
17. Ya zo tare da mutum dubu (1,000) daga kabilar Biliyaminu. Ziba kuma, baran gidan Saul, ya zo a gaggauce a gaban sarki a Urdun tare da 'ya'yansa maza, su goma sha biyar, da barorinsa guda ashirin.
18. Suka haye zuwa wancan hayi don su hawo da iyalin sarki, su kuma yi masa abin da zai ji daɗi.Sa'ad da sarki yake shirin hayewa, sai Shimai ɗan Gera ya zo ya fāɗi a gābansa.
19. Ya ce wa sarki, “Ina roƙon Ubangijina, sarki, in ka yarda kada ka riƙe baranka da laifi, kada ka tuna da laifin da baranka ya yi a ranar da Ubangijina sarki yake gudu daga Urushalima. Kada sarki ya riƙe wannan a zuci.
20. Gama na sani, ranka ya daɗe, na yi laifi, shi ya sa na zama na farko daga gidan Yusufu yau da na fito domin in taryi ubangijina sarki.”
21. Abishai ɗan Zeruya kuwa ya ce, “Ya kamata a kashe Shimai gama ya zagi wanda Ubangiji ya zaɓa ya zama sarki.”
22. Amma Dawuda ya ce wa Abishai da ɗan'uwansa Yowab, “Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Kuna so ku jawo mini wahala? Ni ne Sarkin Isra'ila yanzu, don haka ba Ba'isra'ilen da za a kashe a yau.”
23. Sa'an nan ya ce wa Shimai, “Ina tabbatar maka, cewa, ba za a kashe ka ba.”
24. Sa'an nan Mefiboshet jikan Saul ya gangara ya taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har zuwa ranar da ya komo da nasara Mefiboshet bai wanke ƙafafunsa ba, bai kuma yi gyaran fuska ba, bai ma wanke tufafinsa ba.
25. Sa'ad da ya iso daga Urushalima don ya taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba, Mefiboshet?”