23. Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.
24. Dawuda kuwa ya zo Mahanayim. Absalom kuma da dukan mutanen Isra'ila suka haye Urdun.
25. Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba'isma'ile, wanda ya auri Abigail 'yar Nahash, 'yar'uwar Zeruya mahaifiyar Yowab.
26. Absalom da mutanen Isra'ila suka kafa sansaninsu a ƙasar Gileyad.
27. Sa'ad da Dawuda ya kai Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lodebar, da Barzillai Bagileyade daga Rogelim,
28. suka kawo wa Dawuda da jama'arsa waɗannan kaya da abinci, wato gadaje, da tasoshi, da tukwane, da alkama, da sha'ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa,
29. da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu. Gama sun sani Dawuda da mutanensa suna jin yunwa, da gajiya, da kishi, a cikin jeji.