2 Sam 17:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Zan fāɗa masa sa'ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya, in firgitar da shi. Dukan mutanen da suke tare da shi za su gudu. Shi kaɗai zan kashe.

3. Zan kawo maka dukan jama'a kamar yadda akan kawo amarya a gidan angonta. Ran mutum guda kaɗai kake nema, sauran mutane duka kuwa su yi zamansu lafiya.”

4. Wannan shawara ta gamshi Absalom da dattawan Isra'ila.

5. Sa'an nan Absalom ya ce, “A kirawo Hushai Ba'arkite don mu ji abin da shi kuma zai faɗa.”

2 Sam 17