27. Sa'an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da 'ya'yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata.
28. Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”
29. Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.
30. Dawuda yana tafe ba takalmi a ƙafarsa, ya rufe kansa, yana ta kuka, sa'ad da yake hawan Dutsen Zaitun, dukan mutane kuma da suke tare da shi suka rufe kawunansu, suna hawa, suna kuka.