17. Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”
18. Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar.
19. Tamar ta baɗe kanta da toka, ta keta doguwar rigarta mai hannuwa wadda ta sa, ta rufe fuska da hannu, ta tafi tana ta kuka da ƙarfi.
20. Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta.
21. Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.
22. Amma Absalom bai tanka wa Amnon da wata magana ta alheri ko ta mugunta ba, gama yana ƙin Amnon saboda ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.
23. Bayan shekara biyu cif, sai Absalom ya sa a yi masa sausayar tumaki a Ba'al-hazor, wadda take kusa da Ifraimu. Ya kuma gayyaci dukan 'yan'uwansa, wato 'yan sarki.