2 Sam 12:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.

2. Basaraken yana da garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu.

2 Sam 12