4. Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.
5. Domin ba wa'azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.
6. Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.
7. Wannan wadata da muke da ita kuwa, a cikin kasake take, wato, jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.