2 Kor 4:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka, da yake muna da wannan hidima bisa ga jinƙan Allah, ba za mu karai ba.

2. Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta wurin bayyana gaskiya a fili, sai kowane mutum ya shaidi gaskiyarmu a lamirinsa a gaban Allah.

2 Kor 4