1. Wannan shi ne zai zama zuwana na uku a gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.
2. Na gargaɗi waɗanda suka yi zunubi a dā, da kuma saura duka, a yanzu kuma da ba na nan ina yi musu gargaɗi, kamar yadda na yi sa'ad da nake nan a zuwana na biyu, cewa in na sāke zuwa ba zan sawwaƙe musu ba.