20. Ina tsoro kada watakila in na zo in same ku ba a yadda nake so ba, ku kuma ku gan ni ba a yadda kuke so ba, ko ma a tarar da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da yanke, da tsegunguma, da girmankai, da tashin hankali.
21. Ina tsoro kada in na sāke zuwa, Allahna ya ƙasƙanta ni a gabanku, in kuma yi baƙin ciki saboda waɗansu da yawa da suka yi zunubi a dā, ba su kuwa tuba da aikinsu na lalata ba, da fasikancinsu, da fajircinsu da suka aikata.